Isa ga babban shafi
UEFA-ESL

UEFA za ta dakatar da kungiyoyin da suka amince da gasar ESL

Shugaban hukumar kwallon kafar Turai UEFA, Aleksander Ceferin ya yi barazanar dakatar da kungiyoyin da suka amince da sabuwar gasar European Super League daga shiga gasar cin kofin zakarun Turai, haka zalika haramcin gasar Euro da gasar cin kofin Duniya ga daidaikun ‘yan wasan da suka goyi bayan sabuwar gasar.

Shugaban hukumar kwallon kafar Turai UEFA, Aleksander Ceferin.
Shugaban hukumar kwallon kafar Turai UEFA, Aleksander Ceferin. Richard Juilliart UEFA/AFP
Talla

Ceferin da ke bayani bayan matakin kungiyoyin kwallon kafar Turai 12 na amincewa da gasar ta ESL ya ce gasar za rage karsashi da kimar kwallo ga magoya baya inda ya zargi wasu daidaiku da assasa ta da nufin cika aljihunsu.

Zuwa yanzu Kungiyoyin kwallon kafa 12 ciki har da Barcelona da Real Madrid da Atletico Madrid a Spain da kuma AC Milan da Inter Milan da Juventus a Italiya baya ga Arsenal da Chelsea da Liverpool da Manchester City da Manchester United da Tottenham a Ingila ne suka amince da tayin sabuwar gasar ta ESL.

A Ingila inda batun gasar ya fara yamutsa hazo, ministan al’adu Oliver Dowden ya ce za su fara bibiyar ra’ayoyin magoya baya gabanin daukar mataki akai.

A cewarsa idan har ra’ayoyin magoya baya ya nuna suna bukatar gasar ta ESL gwamnatin a shirye ta ke ta mara baya, sai dai akasin haka zai sanya ta kalubalantar gasar.

Sai dai Akeksander Ceferin da ke mayar da martani ga kalaman na Dowden ya ce kashi 79 na magoya bayan kwallo na kalubalantar gasar wanda ke nuna gwamnatoci basu da hurumin mara baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.