Isa ga babban shafi
Wasanni - Kwallon Kafa

Shugaban Real Madrid ya furta kalamai marasa dadi kan tsaffin 'yan wasansa

Bayanai na ci gaba da fitowa dangane da kalamai marasa dadi da shugaban Real Madrid Florentino Perez ke fadi kan wasu tsaffin fitattun ‘yan wasansa da ma daya daga cikin masu horaswar da suka yi aiki tare.

Florentino Perez shugaban kungiyar Real Madrid.
Florentino Perez shugaban kungiyar Real Madrid. AFP/Archives
Talla

Hira ta baya bayan nan da jaridar El Confidencial da ake wallafata a intanet ta bayyana ita ce wadda Perez ke bayyana tsohon mai tsaron ragarsu Iker Casillas da dan wasan gaba Raul Gonzales a matsayin wadanda suka yiwa kungiyar Real Madrid damfara mafi muni, hirar da yayi tun a shekarar 2006.

A ranar Laraba El Confidencial ta fitar da wata hirar muryar shugaban na Real Madrid da aka nada da yake yin watsi da kimar tsohon dan wasan kungiyar da babu kamarsa Cristiano Ronaldo da kuma tsohon kocinsa Jose Mourinho.

Shugaban Real Madrid Florentino Perez tare gwarzon dan wasan kungiyar Cristiano Ronaldo.
Shugaban Real Madrid Florentino Perez tare gwarzon dan wasan kungiyar Cristiano Ronaldo. JAVIER SORIANO AFP/Archives

Cikin hirar da aka nada a shekarar 2012, an jiyo Perez na bayyanawa wani da ba a san ko waye ba cewar Ronaldo marasa hankali ne la’akari da wasu irin dabi’unsa na rashin nutsuwa, duk da bajintar da ya yiwa kungiyar Real Madrid daga shekarar 2009 zuwa 2018 ciki har da taimaka mata wajen lashe kofunan gasar Zakarun Turai 4.

Perez ya kuma caccaki Jorge Mendes wakilin Ronaldo da kuma tsohon kocinsu Jose Mourinho wanda ya horas da Madrid a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2013.

A cewar Perez Mendes dan kasar Portugal ba shi da tasiri ko kadan kan Mourinho da Ronaldo da yake yiwa dillanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.