Salah ya shiga gaban jerin 'yan wasan Afrika da suka nuna bajinta
‘Yan wasan Afrika sun ci gaba da nuna bajinta a wasan farko na sabuwar kaka inda Mohamed Salah na Masar ya ci gaba da rike kambunsa a matsayin jagora a tsakaninsu bayan kafa tarihin zama dan wasan firimiya da ya zura kwallo a wasan farko na kowacce sabuwar kaka cikin shekaru 5 a jere bayan kwallonsa a karawar Liverpool da Norwich da aka tashi wasa 3 da nema.
Wallafawa ranar:
Sauran ‘yan wasan da suka nuna bajinta a wasan farko na Firimiyar sun hada da Isma’il Sarr na Senegal da ke taka leda a Watford wanda shima ya zura kwallo a wasan da suka yi nasara kan Aston Villa da kwallaye 3 da 2.
Haka zalika akwai Said Benrahma na West Ham wanda shima ya taimakawa kungiyarsa nasara kan Newcastle da kwallaye 4 da 2.
Sauran ‘yan wasan Afrika da suka nuna bajinta a karshen makon sun hada da Yousef en Nasriy na Morocco da ke taka leda da Sevilla karkashin gasar Laliga sai Oussama Idriss shima dai dan Maroccon a Sevilla wadanda dukkaninsu suka yi rawar gani a wasan na jiya.
Akwai kuma Taiwo Awoniyi dan Najeriya da ke taka leda a Union Berlin karkashin gasar Bundesliga wanda shima ya zura kwallo guda a wasan da suka tashi kunnen doki da Bayer Leverkusen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu