Thibaut Courtois ya tsawaita kwantiraginsa da Real Madrid zuwa 2026
Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois ya amince da sabunta kwantiraginsa zuwa karin shekaru 5 a nan gaba wato har nan da watan Yunin 2026.
Wallafawa ranar:
Courtois dan Belgium mai shekaru 29 wanda ya koma Madrid daga Chelsea tun cikin shekarar 2018 kan farashin yuro miliyan 35 ya taka rawar gani a kungiyar mai doka La Liga cikin shekaru ukun baya-bayan nan.
Wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter da yammacin jiya litinin Courtois ya ce wannan kakar wasan za ta zama ta hudu ya na taka leda a club din da ya ke matukar kauna.
A cewar mai tsaron ragar babbar dama ce gare shi iya ci gaba da taka leda da Real Madrid yayinda ya yi fatan dorawa kan kwazon da ya nuna a kakar da ta gabata.
Courtois wanda zuwa yanzu ya yiwa Madrid wasanni 100 bayan nasarar kungiyar a karawarsu da Alaves ranar asabar din da ta gabata, ya ce yana da yakinin samun damar tsawaita kwantiragin na sa na da nasaba da kwazonsa a kakar da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu