paraguay - wasanni
Paraguay ta kori kocinta bayan shan kashi a hannun Bolivia
Paraguay ta kori kocin ta Eduardo Berizzo dan kasar Argentina bayan da Bolivia ta lallasa su da ci 4-0 a wasan neman gurbi a gasar cin kofin duniya.
Wallafawa ranar:
Talla
Nasarar da aka yi a kan Paraguay a wasansu na jiya Alhamis ta bar kasar amatsayin ta takwas a wasannin na sharen fagen shiga gasar neman cin kofin duniya da Qatar zata karbi bakwanci a badi, inda ake daukar kashe hudu a kowane yanki.
Hukumar kwallon kafar Paraguay ta ce” cikin kwanaki masu zuwa za ta sanar da sabon mai horar da tawagar kasar."
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu