Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Carrick zai ja ragamar Manchester United bayan korar Solskjear

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ce sai nan da karshen kakar wasan da muke ciki ne za ta sanar da magajin Ole Gunnar Solskjear bayan raba gari da manajan na ta a asabar din nan sakamakon shan kayen da kungiyar ta yi da kwallaye 4 da 1 a hannun Watford.

Manajan Manchester United na wucin gadi, Michael Carrick tsohon dan wasan kungiyar da ya dage mata kofuna 18 a kaka 12 da ya shafe yana taka leda.
Manajan Manchester United na wucin gadi, Michael Carrick tsohon dan wasan kungiyar da ya dage mata kofuna 18 a kaka 12 da ya shafe yana taka leda. AFP/File
Talla

Kafin shan kayen na asabar mai cike da abin kunya dai, United ta sha makamancin kayen har gida a hannun Liverpool da Manchester City cikin makwannin nan, wanda ya fusata magoya bayanta matuka.

Sanarwar da United ta wallafa a shafinta ta bayyana sunan Michael Carrick tsohon dan wasanta na tsakiya kuma wanda ke aiki cikin tawagar masu horarwa na kungiyar a matsayin wanda zai ja ragamar tawagar na wucin gadi har zuwa karshen kaka.

Manchester United ta godewa Solskjear kan kokarin da ya yiwa kungiyar sai dai ta ce abin takaici ne yadda aka kawo wannan mataki mai cike da abin kunya.

Korar ta Solskjear ta kawo karshen shekaru 3 da mai horarwar dan Norway ya shafe ya na jagorancin kungiyar ba tare da kofi ko daya ba.

Yanzu haka dai United ke matsayin ta 8 a teburin Firimiya tazarar maki 12 tsakaninta da Chelsea jagora.

Wasan farko da Carrick zai jagoranci United shi ne haduwarta da Villarreal a talatar nan.

Tuni dai aka fara rade-radin manajan da United ke harin dauka a karshen kakar ciki kuwa har da Mauricio Pochettino na PSG da kuma Zindine Zidane baya ga Brendan Rodgers na Lester City ko kuma manajan Ajax Eric ten Hag.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.