Isa ga babban shafi
Wasanni

United ta tuntubi tsohon kocin Schalke 04

Rahotanni daga majiyoyi kwarara sun ce Manchester United na shirin nada tsohon kocin kungiyar Schalke 04 Ralf Rangnick a matsayin mai horas da ‘yan wasanta na wucin gadi har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Tsohon kocin kungiyar Schalke 04 Ralf Rangnick dake shirin zama mai horas da Manchester United na wucin gadi.
Tsohon kocin kungiyar Schalke 04 Ralf Rangnick dake shirin zama mai horas da Manchester United na wucin gadi. John MACDOUGALL AFP/File
Talla

Wani labari da kafar watsa labaran wasanni ta ‘The Athletic’ ta buga, ya ce Rangnick ya cimma yarjejeniyar karbar aikin horas da ‘yan wasan United na tsawon watanni shida, bayan kammala wa’adin kuma zai fara aikin baiwa kungiyar shawarwari na tsawon shekaru biyu.

Ana sa ran aikin Michael Carrick dake zama kocin rikon kwarya a yanzu zai zo karshe bayan karawar da za su yi da Chelsea a ranar Lahadi.

A halin yanzu dai United na matsayi na 8 da maki 17 a teburin gasar Firimiya, maki 12 tsakaninta da Chelsea dake jagorantar gasar ta bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.