Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Jorginho baya bukatar Ballon d'Or don nuna bajintarsa ga Duniya- Tuchel

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel ya ce Jorginho baya bukatar Ballon d’Or gabanin nuna cewa yana jerin zaratan ‘yan kwallo na duniya.

Dan wasan tsakiya na Italiya Jorginho.
Dan wasan tsakiya na Italiya Jorginho. Paul ELLIS AFP/File
Talla

Jorginho dai ya zo na uku ne kasa da Lionel Messi da kuma Robert Lewandowski a jerin ‘yan kwallon da suka shiga tseren lashe kyautar ta Ballon d’Or wadda Messi na PSG ya lashe a karo na 7.

Jorginho ya yi nasarar dagewa Chelsea kofin zakarun Turai yayinda ya taka muhimmiyar rawa wajen kai kofin Euro kasarsa Italiya bayan doke Ingila, nasarorin da ake ganin ya cancanci lashe kyautar.

Tuchel ya ce zai yi fatan Jorginho mai shekaru 29 ya fi mayar da hankali wajen nasarori na jumulla wato ga kasa ko kuma kungiya maimakon kyautukan radin kai.

Acewar Tuchel a wajensa samun nasarar zama kungiya mafi bajinta na shekara yafi kyautar ta Ballon d’Or la’akari da cewa duk wani dan wasa da ya kai ga lashe kyautar to fa kungiyarsa ce ta kaishi matakin ba wai shi kadai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.