Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

UEFA ta dage wasan Tottenham da Lille saboda harbuwar 'yan wasa da corona

Hukumar UEFA ta sanar da dakatar da wasan Tottenham da Rennes yau alhamis karkashin gasar Europa Conference league bayan 8 daga cikin ‘yan wasan kungiyar ta Tottenham sun harbu da cutar corona.

Wasu 'yan wasan Tottenham.
Wasu 'yan wasan Tottenham. Daniel LEAL AFP
Talla

Tun a daren jiya laraba Tottenham ta sanar da kulle sansanin horar da ‘yan wasanta sakamakon harbuwar ‘yan wasa 13 ciki har da wasu daga cikin tawagar masu horarwarta suka yi.

Sai dai Rennes ta Faransa da ke shirin yin tattaki zuwa London tun a jiya ta sanar da matakin na Tottenham dangane da dakatar da wasan a matsayin batu mai rikitarwar.

Amma kuma sanarwar hukumar UEFA ta yau ta amince da dakatar da wasan zuwa wani lokaci a nan gaba ko da ya ke sanarwar ta ce matakin na Tottenham ya sanya ta a tsaka mai wuya.

Acewar UEFA sai a nan gaba ne za ta sanar da mataki na gaba kan yadda wasan kungiyoyin zai gudana, la’akari da cewa a ranar 31 ga watan nan na Disamba ne ake saran Karkare wasannin rukuni na gasar.

Akwai dai yiwuwar Tottenham ta bukaci dakatar da wasanta da Brighton karkashin gasar firimiyar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.