Barcelona za ta hadu da Napoli a Europa bayan ficewa daga gasar zakarun Turai
Barcelona za ta fafata da Napoli a wasan gasar Europa bayan da kungiyar ta rikito daga babbar gasar zakarun Nahiyar Turai ta Champions League a karon farko tun bayan kakar wasa ta 2000 zuwa 2001.
Wallafawa ranar:
Kungiyar, a karkashin mai horarwa Xavi Hernandez za ta ci gaba da gwabzawa a wannan karamar gasar ta zakarun Turai, inda duk wadda ta yi nasara tsakaninta da Napoli za ta wuce zagayen kungiyoyi 16.
Daraktan kwallon kafa na kungiyar Bracelona Mateu Alemany, ya ce lallai Napoli babbar kungiya ce, kuma ‘yan wasanta sun san makaman aiki a fagen tamaula, saboda haka wasan zai yi matukar wahala.
Za a yi zubin farko na wasan ne a filin wasan Barcelona na Camp Nou a ranar 17 ga watan Fabrairun shekarar 2022, sannan Barcelona ta mayar da biki a ranar 24 ga Fabrairun a filin wasan Diego Armando Maradona da ke birnin Naples, wato filin Napoli kenan.
Kungiyoyin biyu sun taba haduwa a zagayen kungiyoyi 16 a gasar zakarun nahiyar Turai ta Champions League a kakar wasa ta 2019-20, inda Barcelona ta yi waje road da Napoli 4-2 jimilla.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu