Isa ga babban shafi
Wasanni

Najeriya ta rasa muhimman 'yan wasa gabanin fara gasar AFCON

Tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta gamu da cikas gabannin fara gasar cin kofin kasashen Afirka nan da lokaci kalilan a Kamaru.

Dan wasan Najeriya Odion Ighalo
Dan wasan Najeriya Odion Ighalo © REUTERS/Sumaya Hisham
Talla

Kalubalen rasa muhimman ‘yan wasa ya sake bijirowa Najeriya ce, bayan da hukumar kwallon kafar kasar ta NFF ta bayyana cewar dan wasan gaba Odion Ighalo ba zai buga gasar AFCON ba, abin da ke nuni da yiwuwar fuskantar koma baya ga yunkurin Najeriya na neman lashe gasar a karo na 4.

Hukumar NFF ta ce Ighalo ba ya cikin tawagar ta ne saboda kin bashi damar komawa gida da kungiyarsa ta Al-Shabab da ke kasar Saudiya ta yi.

Dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar Najeriya Odion Ighalo
Dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar Najeriya Odion Ighalo AFP/File

Dan wasan dai shi ne ya fi zura kwallaye a gasar ta cin kofin kasashen Afirka a shekarar 2019, gasar da Najeriya ta kare a matsayi na uku, kuma idan za a iya tunawa a waccan lokacin ya sanar da matakin yin ritaya daga bugawa kasar tasa kwallo.

Victor Osimhen
Victor Osimhen © REUTERS/Mohamed Abd El Ghany

A makon da ya gabata ne hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta tabbatar da cewa fitaccen matashin dan wasan kasar na gaba mafi tsada a Afirka, da ke taka leda a kungiyar Napoli wato Victor Osimhen, ba zai buga gasar cin kofin kasashen Afirka ba, saboda matsalar lafiya, duk da cewar dan wasan ya bayyana a shirye yake ya buga gasar AFCON a Kamaru, la’akari da cewar ya murmure daga raunin da ya samu a kansa, yayin wani wasa da ya bugawa Napoli a gasar Seria A a cikin watan Nuwamba.

Wasu karin bayanai kuma sun tabbatar da cewa, baya ga Osimhen, kungiyar Watford da ke Ingila, ta ki sakin dan wasanta na gaba dan asalin Najeriya, Dennis Emmanuel, matakin da hukumar NFF ta bayyana bacin ranta akai.

Dan wasan baya ma dai Leon Balogun da Abdullahi Shehu dake wasa a kasar Cyprus ma suna cikin ‘yan wasan da aka haramtawa wakiltar Najeriya a Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.