Isa ga babban shafi
Wasanni

Pogba ya musanta rahoton yi masa tayin albashin fam dubu 500 a mako

Dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba ya yi watsi da rahotannin da ke cewa kungiyar ta gabatar masa da tayin biyansa fam dubu 500 duk mako, abinda zai sanya shi zama dan wasan da ya fi karbar albashi a gasar Firimiya, domin ka da ya sauya sheka.

Paul Pogba
Paul Pogba Adrian DENNIS AFP
Talla

A ranar Juma’ar da ta gabata, rahotanni suka bayyana cewa shugabannin United sun yi yunkurin karshe na shawo kan Pogba ya ci gaba da zama a kungiyar kuma sun shirya mayar da shi dan wasa mafi yawan albashi a tarihin Firimiya.

Cikin wannan shekara ta 2022 yarjejeniyar Pogba da Manchester United za ta kare.

Yanzu haka dai Pogba na cikin watanni shida na karshe a yarjejeniyarsa da Manchester United bayan da ya ki amincewa da tattaunawa kan tsawaita zamansa a kungiyar.

Kungiyoyin Real Madrid da Paris Saint-Germain da Juventus ne kungiyoyin da ke kan gaba a Turai wajen fatan sayen dan wasan na Faransa kafin ko kuma a lokacin sabuwar kakar wasanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.