Isa ga babban shafi
Najeriya - Wasanni

Kaftin din Super Eagles ya nemi afuwar 'yan Najeriya

Kaftin din kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya Ahmed Musa ya nemi gafarar magoya bayan su dangane da gazawar da suka yi lokacin karawa da kasar Tunisia a gasar cin kofin Afirka dake gudana a kasar Kamaru.

Kaftin din tawagar Najeriya Ahmed Musa da dan wasan Algeria Riyad Mahrez, yayin wasa a Masar 14/07/2019.
Kaftin din tawagar Najeriya Ahmed Musa da dan wasan Algeria Riyad Mahrez, yayin wasa a Masar 14/07/2019. AP - Ariel Schalit
Talla

A sakon da ya aikewa ‘Yan Najeriya a shafin sa na Facebook, Musa yace a rayuwa ba koda yaushe ake samun abinda ake so ba, saboda haka ya dace ayi hakuri akai.

Kaftin yace sun bada kashi 100 na abinda za su iya yi wajen samun nasarar wasan, amma kuma basu samu nasarar da ake bukata ba.

Musa yace ba za suyi kasa a gwuiwa ba a gasa ta gaba, yayin da ya godewa ‘Yan Najeriya akan irin goyan baya da addu’oin da suka yi ta musu.

Kasar Tunisia ta doke Najeriya da ci 1-0 a zagaye na biyu na gasar cin kofin Afirka dake gudana a Kamaru, abinda yayi sanadiyar fitar kasar daga gasar.

Ana saran Najeriya ta kara da Ghana a zagayen karshe na neman tikitin zuwa cin kofin duniya a watan Marin mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.