Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

'Yan wasan Kamaru sun bayar da albashinsu ga wadanda turmitsin Olembe ya shafa

‘Yan wasan tawagar kwallon kafar Kamaru sun bukaci shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Samuel Eto’a ya bai wa wadanda turmitsitsin filin wasa na Olembe ya ritsa da su a Yaounde ranar Litinin da ta wuce kudaden da aka alkawarta za a ba su sakamakon ketarawa zuwa zagaye na biyu na gasar AFCON.

Cameroon's national football team: the 'Indomitable Lions'
Cameroon's national football team: the 'Indomitable Lions' Issouf SANOGO AFP
Talla

Magoya baya 8 ne suka mutu, kana 38 suka ji rauni, 7 daga cikinsu munanan raunuka, bayan turmitsitsin da ya auku  a wajen filin wasa na Olembe, gabanin wasan kungiyoyin 16 na karshe tsakanin Kamaru da Comoros.

Kowane dan wasan Kamaru zai karbi dala dubu 85 sakamakon kai wa matakin sili daya kwale na gasar ta AFCON.

kakakin tawagar kwallon kafar Kamarun, Serge Leopold, wanda  sanar da haka ya ce tuni Eto’o ya amince da wannan bukata ta ‘yan wasan.

Kamaru ta sadaukar da nasarar da ta samu a kan Gambia a wasan daf da na karshe na ranar Asabar da ta gabata ga wadanda wannan iftila’i ya rutsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.