Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Akwai yiwuwar Sadio Mane ya raba gari da Liverpool- rahoto

Wasu bayanai na cewa da yiwuwar zakaran Afrika Sadio Mane ya raba gari da kungiyarsa ta Liverpool zuwa La Ligar Spain dai dai lokacin da ya ke da ragowar watanni 18 a kwantiragin da ke tsakaninsa da Reds.

Sadio Mané bayan dage kofin Afrika.
Sadio Mané bayan dage kofin Afrika. CHARLY TRIBALLEAU AFP
Talla

Jaridai wasanni ta goal ta yi ikirarin cewa, Mane ya shaidawa dillalinsa cewa zai mutunta ta yi daga Barcelona ko Real Madrid don cika burinsa na yarinta wajen kammala wasanninsa a La Ligar Spain.

Mane wanda tun bayan komawarsa Liverpool daga Southampton a 2016 ya dage kofunan Firimiya da na zakarun turai da kuma kofin duniya na kungiyoyi, gabanin kofin Afrika a watan nan, yanayin zubin ‘yan wasan da Jurgen Klopp ke amfani da shi a yanzu na nuna yiwuwar dan wasan na Senegal ya rasa gurbi kamar a baya.

Idan har ya tabbata Mane ya samu damar komawa La Liga daga Firimiyar Ingila, kenan ya bi sahun zaratan ‘yan wasan Afrika irinsu Samuel Eto da Yaya Toure da suka dauki irin wannan mataki a karshen taka ledarsu.

Har zuwa yanzu dai Mane bai koma Liverpool ba wanda ke nuna zai rasa karawar kungiyar ta gobe Alhamis da Leicester City karkashin firimiya, koda ya ke da yiwuwar ya samu karawar ranar lahadi inda kungiyar tasa za ta yi tattaki zuwa Burnley.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.