Pele zai ci ga da kasancewa a asibiti saboda cutar mafitsara
Shahararren dan wasan kwallon kafar nan dan kasar Brazil, Pele, zai ci gaba da kasancewa a asibiti a birnin Sao Paulo sakamakon sanyin mafitsara, inda tun da farko ake masa maganin sankarar hanji, kamar yadda hukumomin asibitin suka bayyana a Litinin.
Wallafawa ranar:
Tun da farko an kwantar da tsohon dan wasan mai shekaru 81, wanda ake wa inkiya da ‘O Rei’, wato sarki a asibin Albert Einstein na birnin Sao Paulo ne a ranar 13 ga watan Fabrairu don ci gaba da yi masa aganin lallurar hanji da yake fama da ita, wadda aka gano a watan Satumban shekarar da ta gabata.
Kwanaki 8 bayan an kwantar da shi ne likitoci suka ce sun gano sanyin mafitsara a tattare da shi, lamarin da zai tsawaita zamansa a asibitin.
Wannan ne lallaurar rashin lafiya ta baya bayan nan da ta addabi tsohon dan wasan mai yawan shekaru, wanda bayyanarsa a bainar jama’a yake ci gaba da raguwa.
Dan wasan da ake ganin babu irinsa a duniya, wanda aininnhin sunansa Edson Arantes do Nascimento, shine dan wasa daya da ya taba lashe kofunan duniya har 3.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu