Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon Kafa

Liverpool ta lashe kofin Carabao karo na 9 bayan doke Chelsea a fenariti

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi nasarar dage kofin kalubale na Carabao a daren jiya lahadi bayan lallasa Chelsea a bugun fenariti.

'Yan wasan Liverpool.
'Yan wasan Liverpool. POOL/AFP/Archives
Talla

An dai kammala sa’o’I 90 na wasan ba tare da zura kwallo ba sakamakon yadda na’urar VAR ta soke kwallaye 4 saboda offside, wanda ya sanya kara mintuna 30 shima dai ba tare da zura kwallon ba, dalilin da ya bayar da damar doka fenariti wadda shi dinma dai aka doka 10-10, gabanin akai ga bugun mai tsaron raga da mai tsaron raga, inda Kelleher na Liverpool ya yi nasarar yayinda Kepa Arrizabalaga na Chelsea ya gaza zura tasa kwallon.

Mai horar da tawagar Chelsea Thomas Tuchel dai ya gamu da kakkausar suka saboda yadda ya sauya mai tsaron raga Edouard Mendy zuwa Kepa a kasa da minti 1 gabanin tafiya bugun na fenariti, duk da yadda Mendi ya doka mintuna 120 na wasan.

Tuchel dai na kallon Kepa a matsayin gwani ta bangaren bugun fenariti amma kuma sai ya bayyana ta hannunsa ne tawagar ta samu nakasu a jiyan kwatankwacin dai abin da ya faru a 2019 yayin haduwarsu da Manchester City.

Kofin na Carabao dai shi ne karo na 9 da zuwa yanzu Liverpool ta lashe, yayinda kuma ta ke harin kofunan Firimiya da na FA a wannan kaka.

Yayin wasan na jiya dai kungiyoyin biyu makwabtan juna a teburin Firimiya sun nuna goyon baya ga Ukraine da fama da yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.