Isa ga babban shafi
Rasha - wasanni

Rasha za ta shigar da kara kan dakatarwar FIFA da UEFA

Hukumar kwallon kafar Rasha (RFU) ta sanar da shirin daukaka kara a gaban kotun sauraron kararrakin wasanni (CAS) kan korar da aka yi mata daga gasar cin kofin duniya ta 2022 da kuma duk wasu wasannin kasa da kasa.

Shugaban kasar Rasha Vlamir Putin da Infantino na hukumar FIFA
Shugaban kasar Rasha Vlamir Putin da Infantino na hukumar FIFA AFP
Talla

A ranar 24 ga watan Maris ne Rasha ke shirin karawa da Poland a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya, Sai dai a ranar 28 ga watan Fabrairu, FIFA da UEFA suka sanar da haramtawa kasar shiga duk wata gasa sakamakon mamayar da ta yi wa Ukraine.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kusa da kambun kofin duniya tare da shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino a shekarar 2018.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kusa da kambun kofin duniya tare da shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino a shekarar 2018. AFP - ALEXEY NIKOLSKY

A cikin wata sanarwa da ta fitar a cikin harshen Rashanci, Hukumar kwallon kafar kasar ta ce ta na shirin gabatar da kara kan hukumomin kwallon kafar duniya da na Turai don neman a maido da dukkan kungiyoyin kwallon kafar Rasha maza da mata cikin wasannin, tare da bukatar neman diyya kan dakatarwar.

A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da UEFA suka sanar da korar kasar Rasha daga dukkannin wasannin kwallon kafa na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.