Isa ga babban shafi
Wasanni - FA

Chelsea zata hadu da Liverpool a wasan karshe na kofin FA

Chelsea za ta yi haduwa karo na biyu a Wembley da Liverpool a kakar wasa ta bana bayan da ta doke Crystal Palace da ta nuna juriya da ci 2 – 0 ta kuma haye wasan karshe na cin kofin FA.

Ruben Loftus-Cheek yayin murnar zura kwallo a ragar Crystal Palace a wasan kusa da na karshe da Chelsea ta yi nasara 17/04/22.
Ruben Loftus-Cheek yayin murnar zura kwallo a ragar Crystal Palace a wasan kusa da na karshe da Chelsea ta yi nasara 17/04/22. REUTERS - DAVID KLEIN
Talla

Liverpool ta lashe gasar kofin Carabao a bugun fenariti a watan Fabrairu amma wata kila Chelsea ta samu damar ramawa a haduwar da zasu yi a wasan karsha na kofin FA.

Karo na uku kenan a jere Chelsea ke kaiwa wasan karshe na cin kofin FA, sai dai tana fatan tarihi a sauya a wannan karo, bayan ta sha kashi a haduwar biyu da suka gabata a hannun Arsenal da Leicester City.

Kociyan kungiyar Thomas Tuchel na da gagarumin tarihi wajen kaiwa ga wasan karshe na gida da na Turai tun bayan zuwansa Chelsea, yayin da ta kasance babbar abokiyar hamayyar Liverpool, wanda ke neman kofin karo na hudu mai tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.