Isa ga babban shafi

Arsenal ta farfado da fatanta na halartar gasar zakarun Turai

Arsenal ta sake farfado da fatanta na kammala gasar Firimiya ta bana a tsakanin kungiyoyi hudu na farko , abinda zai ba ta damar halartar gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta badi, bayan doke Chelsea da kwallaye 4-2 har gida.

'Yan wasan Arsenal yayin murnar lallasa Chelsea da kwallaye 4-2.
'Yan wasan Arsenal yayin murnar lallasa Chelsea da kwallaye 4-2. Pool via REUTERS - ANDREW BOYERS
Talla

Yan wasan “The Gunners” da suka hada da Eddie Nketiah, da Bukayo saka da kuma Emile Smith Row ne suka taka muhimmiyar rawar ci wa Arsenal kwallaye hudun da ta lallasa Chelsea da su a wasan da suka kara a dare jiya.

Nketiah mai shekaru 22 ne ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea kafin daga bisani Timo Werner ya rama, Emile Smith Rowe ya sake ci wa Arsenal kwallo ta biyu, nan da nan kuma Cesar Azpilicueta ya sake ramawa Chelsea.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma Nketiah ya sake cin kwallonsa ta biyu, ta amma ta uku ga Arsenal, sannan Bukayo Saka ya ci ta hudu.

Yanzu haka Arsenal tana matsayi na biyar a gasar Firimiya, bayan Tottenham ta hudu, dukkaninsu da 57-57, sai dai banbancin kwallaye, yayin da ya rage sauran wasanni shida a karkare kakar wasa ta bana.

A halin yanzu kuma maki 5 ne kawai tsakanin Arsenal da Chelsea wadad ke matsayi na uku da maki 62.

A wasu daga cikin wasannin da aka buga a jiya, Manchester City ta lallasa Brighton da kwallaye 3-0, an kuma tashi 1-1 tsakanin Everton da Leicester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.