Isa ga babban shafi

Benzema ya yi barin kwallaye biyu a karawarsu da Osasuna

Tauraron Real Madrid Karim Benzema ya barar da damar bugun fanareti har sau biyu, yayin karawarsu da kungiyar Osasuna jiya Laraba gasar LaLiga.

Karim Benzema.
Karim Benzema. REUTERS - JUAN MEDINA
Talla

Benzema ya barar da damar cin kwallayen biyu ne kuma cikin mintuna bakwai yayin wasan da suka doke Osasunan da kwallaye 3-1, nasarar da ta baiwa Real Madrid damar kara kusantar lashe kofin gasar LaLiga ta bana.

David Alaba, da Marco Asensio da kuma Lucas Vazquez ne suka ci wa Madrid kwallayenta uku, yayin da Darko Barasanac ya ciwa Osasuna guda.

A halin yanzu Madrid na da maki 78 inda ta baiwa mai biye da ita ta biyu Atletico Madrid mai mai 61 tazarar maki 17 a teburin LaLiga, bayan da Atleticon ta tashi canjaras 0-0 babu ci tsakaninta da Granada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.