Isa ga babban shafi

United za ta hankalin 'yan wasa ko da ba ta gasar zakarun Turai - Rangnick

Kocin rikon kwarya na Manchester United, Ralf Rangnick, ya ce kungiyar za ta ja ra’ayoyin fitattun ‘yan wasa, ko da kuwa sun kasa samun gurbin shiga gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

Kocin Manchester United Ralf Rangnick.
Kocin Manchester United Ralf Rangnick. REUTERS - PHIL NOBLE
Talla

Yayin tsokaci a baya bayan nan kan halin da kungiyar ke ciki Rangnick ya ce ko shakkah babu za su fi son a ce  sun  buga gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa, amma wannan kuma matsalar rashin tabbas dangane da halartar gasar ta shafi sauran kungiyoyi, ba kawai Man United ba.

Yanzu haka dai, kungiyar na bukatar share tazarar maki shida kafin shiga rukunin kungiyoyi hudu na farko a gasar Firimiyar bana, wadda ya rage wasanni hudu a karkareta.

United ta samu nasara a wasanni hudu kacal cikin 15 da ta buga a watannin baya bayan nan, kuma za ta karbi bakuncin Chelsea a filin wasa na Old Trafford a yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.