Isa ga babban shafi
Gasar Premier

Ronaldo ya ci kwallonsa ta 17 a kakar wasa ta bana

Cristiano Ronaldo ya ci kwallonsa ta 17 a kakar wasa ta bana inda ya taimakawa Manchester United samun maki daya, yayin da David de Gea ya sanya Chelsea cikin takaici na tare kwallaye da dama, a wasan gasar Frimiya da suka yi 1 – 1.

Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo.
Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo. © AFP - OLI SCARFF
Talla

Chelsea ta yi kokari sosai a farkon rabin lokaci a Old Trafford, sai dai De Gea ya hanata kaiwa ga gaci duk da matsin lamba daga Kai Havertz da N'Golo Kante.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Chelsea ta zura kwallon ta hannun Marcos Alonso a mintuna na 60, mintuna biyu tsakani Ronaldo ya farke da taimakon Nemanja Matic.

Hakan ya dan kwantar da hankulan ‘yan kallo a Old Trafford mai cike da rudani da rashin tabbas, kan rashin gamsuwa da masu kulob yayin da aka gudanar da zanga-zangar a waje a wasan gida na biyu a jere.

Chelsea taci gaba da burin na neman kammala gasar cikin hudun sama, inda yanzu haka Tawagar Thomas Tuchel tana matsayi na uku da maki 66, takwas a gaban Tottenham mai matsayi na biyar, yayin da ya rage saura wasanni biyar.

Manchester United tana matsayi na shida da maki 55, biyar tsakaninta da Arsenal dake matsayi na hudu amma ta buga wasanni biyu. Man City na saman Teburi da maki 80, maki daya tsakaninta da Liverpool dake biye mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.