Marseille na daf da samun gurbi a gasar zakarun Turai
Marseille ta koma matsayi na 2 a gasar Ligue 1 a jiya Lahadi bayan da ta lallasa Lorient da ci 3-1, lamarin da ya saka ta turbar gasar zakarun nahiyar Turai a kaka mai zuwa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yaran Jorge Sampaoli sun gaza shiga matakin wasan karshe na gasar nahiyar Turai ta Conference League a ranar Alhamis, sakamakon taka musu birki da Feyenoord suka yi, amma sai gashi yanzu su na hanyar shiga babbr gasar Turai ki tsaye.
Kwallaye daga Bamba Dieng, Matteo Guendouzi da Gerson ne suka bai wa Marseille wannan nasara mai matukar mahimanci da suka samu.
PSG, wadanda suka riga suka lashe gasar Ligue 1 ta Faransa, sun buda canjaras 2-2 da Troyes, wadanda su ma malakin kamfaanin nan na Abu Dhabi ne kamar Manchester City.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu