Isa ga babban shafi

Jurgen Klopp na Liverpool ya zama gwarzon manajan Premier League na bana

An zabi Jurgen Klopp na Liverpool a matsayin Gwarzon cocin gasar Premier kaka da aka karkakre, sakamakon rawar da kungiyar ta taka a kakar da kuma lashe kofin FA, bayan da ta doke Chelsea a bugun daga kai sai mai tsaron gida a Wembley.

Kocin Liverpool dan kasar Jamus Jurgen Klopp ya zama kocin Premier League na bana
Kocin Liverpool dan kasar Jamus Jurgen Klopp ya zama kocin Premier League na bana POOL/AFP/File
Talla

Amma Liverpool ta sha kashi a hannun Manchester City da maki daya kacal bayan da 'yan wasan Klopp da na Pep Guardiola suka yi nasara a wasanninsu a ranar Lahadi ta karshe na gasar Premier Ingila.

A jawabinsa na karbar lambar yabon yayin liyafar cin abincin dare na kungiyar Manajojin a Landan ranar Talata, Klop ya ce: "Abin alfahari ne lashe kambin a kakar mai tsarkakiya.

Bajamushen, mai shekaru 54, ya lashe kofin  Sir Alex Ferguson, wanda daukacin mambobi na kungiyar manajoji ke zaba a dukkan sassa don girmama tsohon kociyan Manchester United mai farin jini.

Sauran 'yan takara

Kocin City Pep Guardiola da Thomas Frank na Brentford da Eddie Howe na Newcastle da Patrick Vieira na Crystal Palace na daga cikin jerin sunayen manajojin gasar Premier da aka zaba.

City ta haramtawa Liverpool kafa tarihin lashe kofunan har hudu da babu wanda babu wanda ya taba yi, to amma watakila ta wuce haushi kan Real Madrid a gamuwar da zasuyi ranar asabar a birnin Paris a wasan karshe na gasar zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.