Isa ga babban shafi

Zakarun Turai: Magoya bayan Liverpool dubu 40 sun shiga Faransa babu tikiti

Hukumar kwallon kafar Faransa ta ce marasa tikiti ko kuma masu tikitin jabu 35,000 suka yi yunkurin shiga filin wasa na ‘Stade de France’ a karshen mako domin kallon wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar Turai da aka buga tsakanin kungiyar Real Madrid da Liverpool.

Wasu magoya bayan Liverpool da aka hana shiga kallon wasan karshe na cin kofin zakarun Turai.
Wasu magoya bayan Liverpool da aka hana shiga kallon wasan karshe na cin kofin zakarun Turai. © AFP - THOMAS COEX
Talla

Hukumar ta ce ta sanya jami’an tsaro da masu duba tikiti 1,650 ne domin fargabar samun irin wadannan 'yan kallon da su ke zuwa filaye ba tare da tikiti ba ko kuma dauke da tikitin jabu.

Faransa ta ce tikiti 75,000 aka ware domin 'yan kallon wasan da Real Madrid ta doke Liverpool da ci 1-0, yayinda mutane 110,000 suka je filin wasan da ke arewacin Paris kamar yadda binciken ta ya gano.

Alkaluman da hukumar ta gabatar ya nuna cewar mutane 79,000 suka hau ababan hawa zuwa filin, yayinda 21,000 da suka hada da magoya bayan kungiyoyi da abokan hulda da kuma wadanda UEFA ta gayyata suka isa filin a motocin bas, sai kuma 6,000 da suka yi amfani da tasi, sai kuma 4,100 da suka je filin da motocin su.

Binciken Hukumar ya ce akalla mutane 35,000 suka isa filin ba tare da tikiti ba ko kuma suke dauke da tikitin bogi, abinda ya haifar da matsala wajen samun damar shiga filin abinda ya sa aka jinkirta was an an kusan sa’a guda.

Ministan cikin gida Gerard Darmanin ya jaddada cewar akwai magoya bayan Liverpool tsakanin 30,000 zuwa 40,000 da suka je filin ba tare da tikiti ba, abinda ya sa Yan Sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin kawar da su daga kofofin shiga filin.

Sai dai gwamnatin Birtaniya taki amincewa da zargin, inda ta gabatar da korafi akan yadda aka yiwa magoya bayan Liverpool.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.