Isa ga babban shafi

PSG na gab da kulla kwantiragi da Zidane don maye gurbin Pochettino

Kungiyar PSG na kasar Faransa na gab da cimma yarjejeniya da Zinedine Zidane a matsayin sabon cocinta da zai maye gurbin Mauricio Pochettino.

Tsohon mai horos da 'yan wasan Real Madrid Zinedine Zidane.
Tsohon mai horos da 'yan wasan Real Madrid Zinedine Zidane. AP - Martin Meissner
Talla

A cewar gidan radiyon Europe 1, kungiyar na kan tattaunawa domin tsohon kocin na Real Madrid mai shekaru 49 ya koma PSG kafin sabuwar kakar wasanni.

Da Kamfanin dillancin labaran AFP ya tuntubi majiyar PSG, ta ki amincewa ko ta musanta rahotannin.

Kwantiragin Pochettino bai kare ba

Pochettino dai yana da sauran shekara guda kan kwantiraginsa da PSG kuma ya jagoranci kungiyar da Qatar ke marawa baya  samun nasara a gasar Ligue 1 a kakar da aka Karkare, to amma Real Madrid ta fitar da su daga gasar zakarun Turai a zagaye na ‘yan 16.

Burin lashe Gasar Zakarun Turai

Masu kulob din na Qatar na da burin lashe gasar cin kofin kwallon kafa ta Turai kuma Zidane ya jagoranci kungiyar ta Spain ta lashe kofin kaka uku a jere tsakanin 2016 da 2018.

Tsohon dan wasan da ya lashe gasar cin kofin duniya da Faransa a shekarar 1998, Zidane ya lashe gasar zakarun Turai a lokacin da yake dan wasa a Real a 2002.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.