Isa ga babban shafi

Nottingham Forest ta sayo dan wasan Najeriya daga Union Berlin

Kungiyar kwallon kafa ta Nottingham Forest ta sayo dan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda da Union Berlin can a Jamus Taiwo Awoniyi.

Wannan ne karon farko da Nottingham Forest ke sayo dan wasa da farashi mai tsada daga Union Berlin.
Wannan ne karon farko da Nottingham Forest ke sayo dan wasa da farashi mai tsada daga Union Berlin. POOL/AFP
Talla

Awoniyi mai shekaru 24 bayanai sun ce shi ne dan wasan mafi tsada da kungiyar ta Ingila ta taba siyowa a tarihi daga kungiyar mai doka Bundesliga kan yuro miliyan 17.

Awoniyi wanda tuni ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru 5 tsakanin shi da kungiyar, ya ce dama burinsa ne taka leda karkashin gasar firimiyar Ingila.

A kakar da ta gabata Awoniyi ya zurawa Union Berlin kwallaye 20 a wasanni 43 da ya doka mata.

Awoniyi wanda Liverpool ta saya a 2015 amma kuma ya shafe tsawon shekaru a aro ba tare da ya taba taka mata leda ba, gabanin sayar da shi a bara ga Union Berlin kungiyoyin firimiya da dama sun nuna sha’awar sayensa gabanin da kansa ya zabi Nottingham.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.