Falcons ta fuskantar koma baya saboda rashin Oshoala a gasar AWCON
Yayin da tawagar ‘yan matan Najeriya Falcons ke shirin Fuskantar Botswana a wasan da Dole sai ta samu Nasara muddun tana bukatan a ci gaba da dama da ita a gasar ta Morocco, sai ga shi shaharerriyar ‘yar wasan ta Asisat Oshoala ta fice daga gasar
Wallafawa ranar:
Hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta sanar cewa 'yar wasan ta Super Falcons, Oshoala dake taka leda a Barcelona ba za ta samu damar ci gaba da doka wasannin gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a kasar Morocco ba saboda rauni da ta samu.
Ta samu rauni ne a wasan da Falcons ta yi rashin nasara a hannun Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu da ci 2-1 a wasan farko na rukuni na gasar.
Asisat mai shekaru 27 zata koma Barcelona wannan Alhamis, domin karin gwaje-gwaje a gwiwan nata kafin bayyana girman raunin da ta samu da kuma tsawon lokaci da zata yi jinya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu