Isa ga babban shafi

Joe Gomez ya tsawaita yarjejeniyarsa da Liverpool zuwa 2027

Dan wasan Liverpool mai tsaron baya Joe Gomez ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsawaita kwantiraginsa zuwa nan da shekaru 5 masu zuwa da kungiyar.

Joe Gomez mai tsaron baya na Liverpool.
Joe Gomez mai tsaron baya na Liverpool. AFP
Talla

Joe Gomez dan Ingila mai shekaru 25 wanda ya je Liverpool a shekarar 2015 kenan sabuwar yarjejeniyar ta sa za ta kaishi har zuwa nan da shekarar 2027 gabanin karewa.

Gomez wanda a shekarun baya-bayan nan ya ke fama da yawan jinya biyo bayan rauninsa a gwiwa da idon sahu ya dokawa Liverpool wasanni 142 a tsawon shekaru 7 da ya shafe ya na taka leda da kungiyar mai doka gasar Firimiya.

Duk da cewa matashin dan wasan, sau 21 kadai aka ga kafarsa a fili cikin kakar da ta gabata, amma ya samu gagarumar nasarar dage manyan kofuna da kungiyar tasa a shekarun 7 ciki kuwa har da na Zakarun Turai da kofin FA da kuma Carabao da baya ga UEFA super cup kana Club world cup sannan uwa uba kofin firimiya.

Liverpool wadda kofunan Firimiya da na zakarun Turai suka kufce mata a ranar karshe na shirin tattara karfinta don ganin ta kai kofunan biyu gida a kaka mai zuwa ta hanyar zuba kudi wajen sayen manyan 'yan wasa baya ga rike da dama da ta ke da su in banda Divock Origi da Sadio Mane wadanda kungiyar ta gaza rikewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.