Isa ga babban shafi

Barcelona ta kulla yarjejeniya da Raphinha

Barcelona ta sanar da cimma yarjejeniya da Leeds United, domin sayen dan wasan gaba na kungiyar Raphinha, wanda cikakken sunansa shi ne Raphael Dias Belloli.

Sabon dan wasan Barcelona da ta kulla yarjejeniya da shi daga kungiyar Leeds.
Sabon dan wasan Barcelona da ta kulla yarjejeniya da shi daga kungiyar Leeds. AP - Rui Vieira
Talla

Dan wasan mai shekaru 25 ya shafe shekaru 2 tare da Leeds United dake buga gasar Firimiyar Ingila, yayin da a matakin kasa kuma ya bugawa tawagar kwallon kafar Brazil wasanni 9.

Koda yake cikin sanarwar da ta fitar, Barcelona ba ta bayyana adadin kudin da ta biya kan dan wasan ba, wasu majiyoyi sun ce yawansu ya kai kimanin euro miliyan 55, har ma watakila da kari a nan gaba, idan kulliya ta biya kudin sabulu dangane da sayen dan wasan.

A karkashin yarjejeniyar da aka kulla, Raphinha zai bugawa Barcelona wasa har zuwa shekarar 2027.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.