Isa ga babban shafi

CAF ta fitar da sunayen gwarazan 'yan wasan Afirka Maza da Mata

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) ta bayyana sunayen ‘Yan takara uku a rukunin mata da maza da za’a baiwa kyautar gwaro ku gwarzuwar kwallaon kafar Afirka na wannan shekara, yayin bukin karramawar da zai gudana wannan Alhamis a Rabat na kasar Morocco.

Shugaban Hukumar Kwallon kafar Afirka Patrice Motsepe, yayin jawabi ga 'yan jaridu a filin wasa na Ahmadou-Ahidjo dake Yaoundé, 25/01/22.
Shugaban Hukumar Kwallon kafar Afirka Patrice Motsepe, yayin jawabi ga 'yan jaridu a filin wasa na Ahmadou-Ahidjo dake Yaoundé, 25/01/22. AP - Themba Hadebe
Talla

Manyan ‘yan wasan uku sun fito ne daga jerin sunayen wadanda CAF din ta bayyana tun farko cikin maza da mata da dama da aka zaba amatsayin wadanda suka yi fice a Nahiyar a bana.

Mata

A rukunin gwarzuwar ‘yar wasa, wato rukunin Mata Asisat Oshoala ‘yar Najeriya da ta lashe gasar sau hudu tana farautar kambi na biyar. Sai dai kuma tana fuskantar matsananciyar adawa daga Ajara Nchout Njoya 'yar kasar Kamaru da kuma sabuwar 'yar takara Grace Chanda 'yar kasar Zambia.

Maza

A bangaren maza kuwa, dan wasan Masar Mohamed Salah da Sadio Mane (Senegal) za su fafata da golan Senegal Edouard Mendy.

A ranar Asabar ne za a bayyana wanda ya yi nasara yayin  wasan karshe na WAFCON.

Cikakkun jerin sunayen manyan ‘yan wasan Afirka uku da aka zaɓa.

Gwarzuwar ‘Yar  Wasan Shekara (Mata)

Ajara Nchout Njoya (Kamaru da Internazionale Milano)

Asisat Oshoala ( Najeriya da Barcelona)

Grace Chanda (Zambia da BIIK Kazygurt)

Gwarzon Dan Wasan Shekara (Maza)

Edouard Mendy (Chelsea da Senegal)

Mohamed Salah (Masar da Liverpool)

Sadio Mane (Senegal da Bayern Munich)

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.