Isa ga babban shafi

'Yan wasan Firimiya na duba yiwuwar daina durkuson gwiwa daya

Masu rike da mukaman kaftin-kaftin a kungiyoyin da ke doka gasar Firimiyar Ingila na tattaunawa kan makomar matakin durkuson gwiwa guda don karfafa manufar yaki da nuna wariyar launin fata kafin fara buga wasan sabuwar kaka a ranar Juma'a mai zuwa.

Kungiyoyin na durkuson gwiwa guda ne a kokarin yaki da matsalar nuna wariya.
Kungiyoyin na durkuson gwiwa guda ne a kokarin yaki da matsalar nuna wariya. AP - Dmitry Lovetsky
Talla

Tuni dai aka gudanar da taro na farko kan makomar batun ba tare da cimma matsaya ba.

Tun daga watan Yunin 2020 ne 'yan wasa gasar ta Firimiya suka fara dirkuson gwiwa daya a wani yunkuri na dakile matsalar ta nuna wariya da ke kara tsananta.

Sai dai a cikin watan Fabarairun shekarar nan dan wasan gaba na Crystal Palace Wilfried Zaha ya ce ba zai sake sanya gwiwarsa a kasa ba, domin hakan ba shi da tasiri, la’akari da cewar matakin bai kare ‘yan wasa da dama daga fuskantar cin zarafin nuna musu wariyar launi ba.

Tuni dai ‘yan wasan kungiyoyin gasar Championship da dama a Ingila, da suka hada da Derby County, Brentford, Bournemouth da Queens Park Rangers, suka daina durkusawa da gwiwa daya kafin fara buga wasa, bayan ikirarinsu na cewa hakan baya amfanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.