Isa ga babban shafi

Firimiya ta amince da kawo karshen durkuson gwiwa daya a farkon wasanni

Kaftin-Kaftin diin kungiyoyin da ke taka leda karkashin gasar Firimiyar Ingila sun amince da matakin dakatar da durkuson gwiwa daya da ‘yan wasa a farkon kowanne wasa da nufin yakar matsalar nuna wariyar launin fata da ke ci gaba da tsananta a harkokin wasanni.

Wasu 'yan wasan Firimiya yayin durkuson gwiwa 1.
Wasu 'yan wasan Firimiya yayin durkuson gwiwa 1. POOL/AFP
Talla

Tun daga watan Mayun shekarar 2020 ne ‘yan wasan Firimiyar suka faro durkuso kan gwiwa daya don nuna goyon bayansu ga masu zanga-zangar yaki da nuna wariya ta Black Lives Matter da ta barke a sassan Duniya tun bayan kisan da 'yansandan Amurka suka yiwa bakar fata George Floyd.

Bayan taron da kaftin kaftin din kungiyoyin suka gudanar sun cimma matsayar rika irin wannan durkuso kafin buga wasu zagaye na wasanni, da suka hada da na zagayen karshe, da kuma wadanda ake warewa ranaku kebantattu, kamar yadda aka gani kafin fara buga wasan Community Shield da aka kara tsakanin Liverpool da Manchester City a ranar Asabar din da ta gabata.

Tun farko wasu daidaikun 'yan wasa ne suka fara nuna tirjiya kan matakin durkuson wanda suka ce baya amfanarwa ko kadan wajen dakile nuna wariyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.