Isa ga babban shafi

Manchester United za ta sayo Casemiro, PSG da Arsenal na zawarcin sabbin 'yan wasa

Kungiyar kwallon kafa ta PSG da ke Faransa ta nuna sha’awarta na dauko dan wasan tsakiya na Manchester City Bernardo Silva.

Dan wasan Real Madrid Carlos Henrique Casemiro da Manchester United ke harin saya a wannan kaka.
Dan wasan Real Madrid Carlos Henrique Casemiro da Manchester United ke harin saya a wannan kaka. AFP
Talla

A cewar jaridar The Time, kungiyar da ke doka gasar Ligue 1 na son dauko dan wasan a wannan bazara, kuma a shirye ta ke ta biya yuro miliyan 59 akan dan wasan tsakiyar.

Silva dai kwantiragin sa zai kare ne da City a shekarar 2025.

Itama Manchester United ta fara yunkurin dauko dan wasan tsakiya na Real Madrid Casemiro a kudin da za su iya kai yuro miliyan 60.

Dan wasan mai shekaru 30 zai kasance cikin masu amsar albashi mai tsoka idan ya amince da tafiya kungiyar wadda a yanzu ke kasan teburin firimiyar Ingila bayan rashin nasara a dukkanin wasanninta biyu da ta doka.

United dai ta karkata akalar zawarcin Casemiro ne domin magance barakar da tawagar ta Erik ten Hag ke fuskanta, bayan yunkurin ta na dauko Adrien Rabiot daga Juventus ya ci tura.

Casemiro dai ya kasance a Real Madrid tun shekarar 2013, inda ya lashe kofin La Liga uku da na zakarun Turai 5.

A bangare guda itama kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kammala siyan dan wasan gaba na Juventus Line Hurtig.

A makon nan ne dai ake ta yada jita-jita game da cefano dan wasan, toh amma a yanzu dai kungiyar ta tabbatar da siyo shi.

Shi ma dan wasan gaba na Argentina Giovanni Simeone ya kammala komawa Napoli a matsayin aro daga Verona, batun da kungiyoyin biyu suka tabbatar a yau alhamis.

Dan wasan mai shekaru 27 wanda kuma da ne ga mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, zai koma kungiyar ne bayan zura kwallo 17 a tsohuwar kungiyar sa ta Verona.

A cewar kafofin yada labaran Italia, za’a iya tabbatar da kwantiragin sa akan yuro miliyan 12 idan har aka cika dukkanin ka’idoji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.