Isa ga babban shafi

Manchester City na biyan Haaland kusan fam dubu dari 9 kowanne mako- rahoto

Rahotanni na nuni da cewa dan wasan gaba na Manchester City Erling Haaland ya na daukar albashi da ya kai fam dubu dari 8 da 65 duk mako, kamar yadda jaridar wasanni ta ‘Sportmail’ ta ruwaito.

Erling Braut Haaland na daukar tsabar kudi har fam dubu dari 8 da 65 duk mako a Manchester City.
Erling Braut Haaland na daukar tsabar kudi har fam dubu dari 8 da 65 duk mako a Manchester City. © Reuters/Craig Brough
Talla

Shahararren dan wasan na kasar Norway, wanda ya ke hasakawa a gasar Firimiyar Ingila tun da aka sayo shi daga Borussia Dortmund a kan kudi fam miliyan 51, karbar wadannan makudan kudade ne ya mayar da shi dan wasan da ya fi kowa daukar albashi a kasar Ingila da gagarumar tazara.

Rahotanni sun ce dan wasan mai shekaru 22 ya na daukar albashi mafi karanci dai dai da yadda aka tsara wa manyan ‘yan wasa a Etihaad, sai dai akwai wasu alawus alawus da sauransu, wadanda dahir ne, sune suka hadu suka sa albashinsa ya kai dubu dari 8 da 50 na kudin fam din Ingila, wato fam miliyan 45 kenan duk shekara.

A watan Afrilu ne City ta kasa kungiyoyin da ke zawarcin wannan dan wasa, ta kuma dauko shi ya zama nata, inda ya ke ci gaba da nuna bajinta.

Alkaluman da jaridar ta Sportmail ta wallafa sun nuna cewa ba kadai a Ingila, idan aka yi jumullar kudin da Manchester City ke biyan Haaland, dan wasan a yanzu shi ne mafi daukar albashi a Duniyar kwallo.

Kafin yanzu dai dan wasa mafi daukar albashi a Duniya shi ne Cristiano Ronaldo na Portugal sai dai alawus alawus din da City ke biyan Haaland ya sanya matashin dan wasan dara kowanne dan kwallo yawan albashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.