Isa ga babban shafi

Guardiola ya koka da yadda Manchester City ke barar da damar fenariti

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce dole ne kungiyar ta yi gyara a tsarin bugun fenaritinta la’akari da yadda ta ke samun matsala a duk lokacin da ta samu bugun na daga kai sai mai tsaron raga.

Pep Guardiola ya ce wajibi ne 'yan wasan su dage wajen kaucewa barar da damar fenariti musamman karkashin kasar zakarun Turai.
Pep Guardiola ya ce wajibi ne 'yan wasan su dage wajen kaucewa barar da damar fenariti musamman karkashin kasar zakarun Turai. POOL/AFP/File
Talla

Kalaman na Guardiola na zuwa ne bayan Riyad Mahrez ya barar da damar ta bugun fenariti yayin wasan da suka tashi babu kwallo tsakaninsu da Borussia Dortmund jiya talata karkashin gasar zakarun Turai.

Daga 2016 zuwa yanzu bugun fenriti 25 kadai City ta iya nasarar ci cikin bugu 80 data samu karkashin jagorancin Guardiola.

Duk da cewa City ta yi nasarar kammala wasanninta na rukuni matsayin jagora duk da canjaras din na daren jiya wanda itma a bangare guda bai hana Borussia tsallakawa matakin kungiyoyi 16 na gasar ba, amma Guardiola ya ce abin takaici ne yadda suke rashin nasara wajen bugun na fenariti musamman a gasar zakarun Turai.

A cewar Guardiola karkashin jagorancinsa ‘yan wasan sun barar da damar fenariti har sau 25 karkashin gasar zakarun Turai.

Sai dai wasu alkaluma sun nuna cewa ‘yan wasan sun fi karsashi wajen iya nasara a bugun na fenariti karkiashin gasar zakarun Turai fiye da gasar Firimiyar Ingila.

A baya-bayan nan Mahrez ya barar da damar fenariti 3 cikin 4 da ya doka duk da yadda dan wasan a baya ya iya nasara a bugu 9 cikin 10 da doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.