Isa ga babban shafi

Maguire yana cikin tawagar da za ta wakilci Ingila a Kofin duniya

Dan wasan tsakiya na Leicester City, James Madison ya samu shiga tawgar kwallon kafar Ingila mai ‘yan wasa 26 da za ta wakilci kasar a gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar.

Dan wasan baya na Manchester United, Harry Maguire.
Dan wasan baya na Manchester United, Harry Maguire. POOL/AFP/File
Talla

Kocin Ingilan, Gareth Southgate ya kuma sanya dan wasan gaba na Manchester United, Marcus Rashford da na Newcastle, Callum Wilson, sai kuma dan wasan bayan  Manchester City, Kyle Walker da na  Arsenal Ben White.

Sai dai babu dan wasan baya na AC Milan, Fikayo Tomori, da dan wasan gaba na Brentford, Ivan Toney da na West Ham Jarrod Bowen a cikin wannan tawaga.

Ingila za ta fafata da Iran ne a wasan ta na farko a gasar kofin duniya ta bana a ranar 21 ga watan Nuwamba da karfe 1 na rana agogon GMT.

Ingila na rukunin  B tare da Wales da Amurka.

Wani abin da ya bada mamaki shine yadda aka sanya dan wasan baya na Manchester United Harry Maguire a cikin wannan tawaga da kuma na City, Kalvin Phillips, wanda kwanan na ya gama jinyar raunin da ya ji. Jadon Sancho ba ya cikin wannan tawaga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.