Isa ga babban shafi

Ina yin magana ne a duk lokacin da na ga dama - Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya ce zai yi magana ko tsokaci a kan ko ma menene a duk lokacin da ya ga dama, kuma matsalarsa da Manchester United ba za ta shafi tawagar kasarsa ta Portugal ba a gasar cin kofin duniya.

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. © Tom Purslow/Manchester United via Getty Images
Talla

United na amfani da damammaki da suke da su na shari’a a kokarin da suke na kawo karshen kwantiragin Ronaldo, biyo bayan ganawar da aka yi da shi a wata tashar talabijin, inda ya caccaki kungiyarsa ta United.

Ronaldo mai shekaru 37 ya fada a wata hirar talabijin cewa yana ji kamar an ci amanarsa a United, kuma ba ya ganin girman mai horar da kungiyar,  Erik ten Hag.

Dan wasan wanda ya bayyana a taron manema labarai ya ce, dukkannin wadanda suke wasa tare sun san shi sosai, kuma sun san ko wane irin mutum ne shi.

Dan wasan wanda sau 5 yana lashe kyautar gwarzon kwallon kafa ta Ballon d'Or zai jagoranci kasarsa Portugal a wasan farko a matakin rukunin H na gasar kofin duniya da ke gudana a Qatar, inda za su fafata da Ghana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.