Isa ga babban shafi

Faransa ta samu zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya

Kasar Faransa ta samu damar zuwa zagaye na biyu na gasar cin kofin duniyar dake gudana a kasar Qatar sakamakon nasarar da ta samu akan Denmark da ci 2-1

Dan wasan Faransa Kylian Mbappe
Dan wasan Faransa Kylian Mbappe REUTERS - PETER CZIBORRA
Talla

Dan wasan gaba Kylian Mbappe ya zirarawa Faransa kwallayenta guda 2 wadanda suka bata damar samun gurbi a zagaye na gaba, duk da yake tana da sauran wasa daya nan gaba.

Wannan ya kawo adadin kwallayen da Mbappe ya jefa a cikin wannan gasa zuwa 3, sakamakon jefa guda da yayi a wasan da Faransa ta buga da Australia, wanda ta lashe da ci 4-1.

Ana saran Faransa ta buga wasan ta na karshe a wannan rukuni a ranar 30 ga wata da kasar Tunisia, wadda har ya zuwa wannan lokaci bata lashe wasa guda ba.

Faransa dai itace ke rike da kofin wannan gasa sakamakon nasarar da ta samu wajen lashe shi shekaru 4 da suka gabata.

Sauran wasannin da akayi yau sun nuna cewar Australia ta doke Tunisia da ci 1-0, yayin da Poland ta doke Saudi Arabia da ci 2-0.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.