Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Jamus ta samu kwarin gwiwar ci gaba da kasancewa a gasar

Niclas Fullkrug ya bai wa Jamus kwallo mai mahimmanci da ta ba su canjaras  a wasan da suka fafata da Spain a jiya Lahadi a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar a yanzu haka.

Niklas Fullkrug bayan da ya farke wa Jamus kwallon da aka ci ta.
Niklas Fullkrug bayan da ya farke wa Jamus kwallon da aka ci ta. REUTERS - MATTHEW CHILDS
Talla

Jamus sun samu haske a kokarinsu na tsallakawa zuwa zagaye na gaba a wannan gasa, sakamakon rashin nasarar da Japan suka yi a hannun Costa Rica tun da farko a jiya Lahadi.

Yaran na Hansi flick na bukatar doke Costa Rica a wasan karshe na rukunin E, kuma za su yi  fata Japan ba za su bai wa Spain mamaki ba a haduwar da za su yi.

Spain, sun samu kwallonsu na farko ne a minti na 62, bayan da Alvaro Morata, wanda ya shiga bayan hutun rabin lokaci ya yi amfaanni da kwallon da Jordi Alba ya kawo mai kamar yadda ya kamata.

Jamus sun kara azama har sai da dan wasan gabansu, Niklas Fullkrug ya ci musu kwallo daya ana saura minti 7 a tashi wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.