Isa ga babban shafi

FIFA ta baiwa Morocco damar daukar gasar kungiyoyi ta duniya

Hukumar Kwallon kafa ta duniya ta baiwa kasar Morocco damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya na zakarun kungiyoyin kwallon kafa na nahiyoyin kasashen duniya da za’ayi a watan Fabarairu mai zuwa, saboda gamsuwa da rawar da kasar ta taka a Qatar da kuma tsare tsaren ta. 

Yan wasan kasar Morocco
Yan wasan kasar Morocco REUTERS - CARL RECINE
Talla

Shugaban Hukumar Gianni Infantino ya sanar da wannan matakin, yayin da ya bayyana cewar sabon tsarin gasar da zai kunshi kungiyoyi 32 zai fara aiki daga shekarar 2025. 

Infantino yace a shekarun baya sun amince da shirin fadada yawan kungiyoyin da zasu shiga gasar ta duniya wanda zai kunshi kungiyoyi 8 daga Turai, amma sai annobar korona ta hana gudanar da gasar bara a kasar China. 

Shugaban hukumar yace sabon tsarin mai kungiyoyi 32 kamar gasar cin kofin duniya na kasashe zai fara a shekarar 2025. 

A shekarar 2014, Morocco ta dauki nauyin irin wannan gasar wanda kungiyar Real Madrid ta lashe. 

Yanzu haka dai zakarun nahiyoyin duniya sun hada da Flamengo ta Brazil da Al Hilal ta Saudi Arabiya da Wydad Casablanca na Morocco da Seattle Sounders ta Amurka da kuma Auckland City ta kasar New Zealand. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.