Al'ummar Morocco sun tarbi tawagar kasar da ta nuna bajinta a Qatar
Dubun dubatan ‘yan Morocco ne suka fito a babban birnin kasar jiya Talata don tarbara tawagar kwallon kafar kasar da ta isa gida bayan ta taka rawar gaban hantsi a gasar cin kofin duniya da ta gudana a Qatar, inda ta kasance kasar Larabawa ta farko ko Afrika ta farko da ta kai matakin wasan kusa da na karshe a tarihin gasar.
Wallafawa ranar:
‘Yan wasan tawagar a karkashin jagorancin mai horar da su Walid Regragui sun yi ta daga wa jama’a hannu daga budaddiyar motar bas din da ta dauki su ta na zagayawa da su birnin Rabat, bayan da suka baro filin jirgin saman kasar.
Dimbim ‘ya sanda ne, wasu a motoci, wasu a Babura suka yi wa ‘yan wasan rakiya, inda aka saka jiniya tare da kunna fitilu masu haske.
Taron jama’ar sun yi ta jinjina suna daga hannuwa tare da wasa da tirtsitsin wuta.
Wasu da aka gana da su dai sun bayyana fatan cewa tawagar za ta lashe kofin duniya nan gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu