Isa ga babban shafi

Hakimi da Mbappe sun koma atisaye a PSG

Taurarun ‘yan wasan PSG dake Faransa irinsu Acraf Hakimi da Kylian Mbappe sun koma atisaye a kungiyarsu bayan fafatawar da suka yi a gasar cin kofin duniyan da akakammala a karshen mako a kasar Qatar. 

Hakimi da Mbappe a PSG
Hakimi da Mbappe a PSG © PSG
Talla

Hakimi na daga cikin taurarun ‘yan wasan Morocco da suka nuna bajinta a gasar da aka kammala, saboda yadda suka taimakawa kasarsu ta zama kasa ta farko daga Afirka da ta je matakin kusa da na karshe na cin kofin duniya, kafin Faransa ta haramta mata zuwa wasan karshe. 

Kungiyar PSG ta yada hotunan ‘yan wasan da suka halarci atisaye ayau laraba da suka hada da Hakimi da kuma abokin fafatawarsa Mbappe lokacin da suka yi a atisaye a sansaninsu dake Saint-Germain. 

‘Yan wasan PSG da dama sun taka rawa a gasar cikin kofin duniya da akayi a Qatar cikinsu harda Neymer na Brazil da Lionel Messi wanda ya taimakawa kasarsa ta Argentina lashe kofin. 

Kasashen Argentina da Faransa da kuma Morocco duk sun gudanar da bukukuwan tarbar ‘yan wasan da suka wakilcesu a gasar cin kofin duniya a jiya Talata, yayin da gwamnatin Argentina ta mayar da jiya a matsayin ranar hutu. 

Ana saran PSG ta kara da Strasbourg a ranar 28 ga wata a wasan mako na 16 na gasar Ligue 1 kafin daga bisani su wuce kungiyar Lens wadda zasu kara da ita a ranar 1 ga watan Janairu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.