Isa ga babban shafi

CAF ta hukunta Congo saboda laifin karya kan shekarun 'yan wasanta

An tilastawa Jamhuriyar Demokuradiyar Congo janyewa daga taka leda a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika ta ‘yan kasa da shekaru 17 bayan da gwaji ya nuna cewa, 25 daga cikin ‘yan wasan ta 40 duk sun zarta kayyadaddun shekarun da ake bukata. 

Shugaban hukumar kwallon kafar CAF Patrice Motsepe.
Shugaban hukumar kwallon kafar CAF Patrice Motsepe. © Pierre René-Worms
Talla

Wannan ce badakala ta baya-bayan da ta dabaibaiye hukumar kwallon kafar kasar ta Jamhuriyar Demokuradiyar Congo bayan makamanciyarta da ta faru da kasar Kamaru mai masaukin baki. 

Ita ma dai Kamaru, an gano ‘yan wasanta har guda 32 da suka zarta kayyadaddun shekarun  buga gasar neman gurbin shiga gasar ta cin kofin Afrika ta yan kasa da shekaru 17. 

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Kamaru, Samuel Eto’o, shi ne dai ya bada umarnin amfani da na’urar tantance hakikanin shekarun ‘yan wasan gabanin soma gasar. 

Yanzu haka Jamhuriyar Demokuradiyar Congo ta ce, ba ta da wani zabi, illa kawai ta fice daga wannan gasa, ganin cewa, ‘yan wasa 15 kacal suka rage mata da na’ura ta ce sun cancanta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.