Isa ga babban shafi

Mai Liverpool ya ce kungiyarsa ba ta sayarwa ba ce

Mai kungiyar Liverpool John Henry ya musanta cewar yana shirin sayar da kungiyar, duk da cewa a shekarar da ta gabata ya nemi taimakon masu zuba hannun jari don sake karfafa Club din nasa.

Mai kungiyar Liverpool John W. Henry
Mai kungiyar Liverpool John W. Henry REUTERS - PHIL NOBLE
Talla

A cikin watan Nuwamban da ya gabata shugaban na Liverpool ya bayyana aniyar neman karin masu sayen hannayen jarin kungiyar, matakin da ya ce ko shakkah babu zai taimakawa kungiyar.

Idan za a iya tunawa shekaru 13 baya, kamfanin 'Fenway Sports Group' na John Henry, ya lale tsabar kudi fam miliyan 300 ya sayi Liverpool daga hadin gwiwar attijaran Amurka Tom Hicks da George Gillet.

A karkashin sabon shugabancin ne kuma Liverpool ta lashe kofin zakarun nahiyar Turai a 2019, da kuma kofin gasar Firimiya a shekarar 2020, na farko da ta ci bayan shekaru  30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.