Isa ga babban shafi

Morocco na doka wasan sada zumunta da Brazil gabanin zuwa gasar Copa America

Bayan gagarumar nasara mai cike da tarihi da Morocco ta yi a gasar cin kofin Duniya da ya gudana a Qatar tawagar kwallon kafar na tunkarar wani sabin kalubale a karawarta da Brazil yau asabar, wasan da ke zuwa gabanin taka ledar da kasar ta arewacin Afrika za ta yi a gasar Copa America.

Tawagar Morocco bayan nasarar kaiwa wasan gab da na karshe a gasar cin kofin Duniya.
Tawagar Morocco bayan nasarar kaiwa wasan gab da na karshe a gasar cin kofin Duniya. AP - Luca Bruno
Talla

Morocco na karbar bakoncin Brazil a wasan sada zumunta yau asabar, wasan da za a doka a filin wasa na Ibn Batouta da ke Tangier a kasar, wanda ake alakantawa da shirin da kasar ke yi na tunkarar manyan kasashe ciki har da Argentina a gasar Copa America da za ta shiga cikin wannan kaka.

Mai horar da tawagar ta Morocco Walid Regragui a kalamansa gaban manema labarai jiya juma’a gabanin wasan na yau, ya ce haduwarsu da Brazil wadda ta lashe kofin duniya sai 5 a tarihi zai kara musu kwarin gwiwa matuka.

A cewar mai horarwar na Morocco har sai sun fara gwada kwanji da manyan tawagogin kwallo ne za su tabbatar da karfinsu musamman kasashe irin Spain da Portugal da kuma Brazil.

Regragui ya ce ko da sun yi rashin nasara a wasansu da Brazil yau asabar bacin ran mai sauki ne lura da kasancewar wasan na da sada zumunta, kuma haduwar ta yau za ta kara musu kwarin gwiwar tunkarar manyan kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.