Isa ga babban shafi

Man United na shirin kulla sabuwar yarjejeniya da Rashaford

Manchester United na shirin fara tattauna batun sabon kwantiragi da dan wasan gabanta Marcus Rashford gabanin karshen wannan kaka.

Dan wasan gaba na Manchester United, Marcus Rashford.
Dan wasan gaba na Manchester United, Marcus Rashford. AFP/Archives
Talla

United ta biijiro da zabin Karin shekara guda a kwantiragin Rashaford, wanda zai sa ya ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024, amma kuma sun kagara su cimma yarjejeniya ta tsawon lokaci.

Wasu majiyoyi sun ce United za ta so ta cimma yarjejeniya da Rashford a  karshen wannan shekarar, ko kuma a farkon kaka mai zuwa.

Paris Saint Germain ta Faransa ta nuna sha’awar daukar Rashaford a baya, amma ana sa ran dan wasan mai shekaru 25 ya ci gaba da zama a United, inda yake kan ganiyarsa a karkashin mai horarwa Erik Ten Hag.

United na neman dan wasan gaba kafin kaka mai zuwa, sai dai Rashaford yana cikin tsarin mai horarwa, Ten Hag.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.