Isa ga babban shafi

Rashford ya nuna bajinta a karawar Manchester United da Omonia

Erik Ten Hag ya jinjinawa dan wasansa Marcus Rashford kan yadda ya nuna bajinta a wasan gasar cin kofin Europa a karawar da Manchester United ta samu nasara da kyar a kan Omonia Nicosia a daren Alhamis.

Kwallaye 2 Marcus Rashford ya zura a wasan na jiya yayinda ya taimaka aka zura wani kwallo guda.
Kwallaye 2 Marcus Rashford ya zura a wasan na jiya yayinda ya taimaka aka zura wani kwallo guda. AP - Ian Walton
Talla

Kocin United Ten Hag ya saka dan wasan gaban na Ingila ne daga baya a wasan da suka fafata da kungiyar ta kasar Cyprus, inda kuma da shigarsa ya ci kwallaye 2, ya kuma taimaka wa Anthony Martial ya ci guda.

Ten Hag ya ce ya yaba da irin rawar da Rashford ya taka, yana mai cewa ya kara wa tawagar karfi a wasan na daren Alhamis.

Omonia Nicosia sun bada mamaki, inda dan wasan gabansu Karim Ansarifard ya jefa kwallo a ragar Man United, amma Rashaford ya farke cikin minti 8 ya kuma taimaka wa Martial ya ci wata kwallo.

Rashford ya kara wata kwallon kusan karshen wasa, wanda ya mayar da wasan ya zama 3-1, kafin daga bisani Nikolas Panayiotou ya farke daya aka tashi 3-2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.