Isa ga babban shafi

PSG ta fara shirin sayo Marcus Rashford daga Manchester United

Wasu majiyoyi sun ce kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain ta fara tuntubar dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford a kan yiwuwar kulla yarjejeniya da shi don karfafa ‘yan wasanta na gaba.

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford.
Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford. REUTERS/Phil Noble
Talla

Wata jaridar wasanni da ake wallafawa a kasar Faransa ce ta ta samu cikken bayanai kan shirin PSG na kawo Rashford Paris.

Rashford, mai shekaru 24 ya na da sauran shekara guda gabanin karkarewar kwantiraginsa da Manchester United, kana akwai zabin ya yi karin wata shekara guda, abin da ke nukfin cewa shekaru 2 kenan suka rage masa.

Har yanzu dai PSG ba ta fara tattaunawa da Manchester United ba, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.

Da yiwuwar dai Manchester United ta sanya kudi mai yawa kan dan wasan na ta na gaba ko da ya ke wasu bayanai na cewa abu ne mai wuya kungiyar ta sahale raba gari da Rashford cikin sauki.

Sabon kocin PSG Christophe Galtier ya fada a wani taron manema labarai jiya Alhamis cewa ya na bukatar dan wasan gaba da zai kara da Kylian Mbappe, Hugo Ekitike da Pablo Sarabia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.